Jami'in hulda da jama'a na hukumar Mr. Nick Dazan shi ya shaidawa Muryar Amurka a birnin Ado Ekiti fadar gwamnatin Ekiti jiya Alhamis. Yace sun fara tura kayan domin su tabbatar an samu kayan koina a jihar. Da hukumar zaben ta kan jira sai kwana guda da zabe kafin a raba kayan. Amma sau da yawa kayan basa isa har ranar zaben lamarin da kan kaiga rudani da soma yin zaben a makare.
Yayin da ake batun zaben sai gashi jami'an tsaron Najeriya sun hanawa gwamna Musa Kwankwaso na Kano da Amaechi na jihar Rivers da Oshiomole na jihar Edo dukansu 'yan jam'iyyar APC shiga jihar ta Ekiti.
Dangane da hana gwamnonin shiga Ekiti Nick Dazan yace matakin da mahukuntan suka dauka akan gwamnonin ya zo daidai da doka da matsayin da suka cimma lokacin da suka yi gangami da masu ruwa da tsaki na jihar tare da babban sifeton 'yansandan Najeriya. Bayan haka shi babban sifeton 'yansandan yayi kashedi inda yace duk wanda ba dan jihar Ekiti ba ne ya zauna inda yake kada ya shiga jihar.
Ga rahoton Hassana Umar Tambuwal.