Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Aiwatar Da Sabuwar Dokar Rage Cunkoso A Gidajen Yarin Najeriya


Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano
Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano

Hukumomin kula da gidajen yari a Najeriya sun ce tanade-tanaden sabuwar dokar kula da ayyukan gidajen yari da majalisar dokokin kasar ta zartar kuma shugaban kasa ya rattabawa hannu a shekara ta 2019 za ta taimaka.

Sabuwar dokar za ta taimaka wajen rage cunkoson fursunoni, amma sun nanata cewa, akwai bukatar masu ruwa da tsaki su kara kaimi ta wannan fuska.

Kididdiga daga ma’aikatar kula da lamuran cikin gida ta Najeriya ta nuna yawan daurarrun dake cibiyoyin gyaran hali ko gidajen yari daban-daban a fadin kasar ya zarce ka’ida da dubu 11500, lamarin dake tabbatar da yanayin cunkoso a gidajen yarin kasar.

Yanzu haka dai gwamnatin kasar na gina sabon gidan yari a Kano da zai dauki yawan daurarru dubu uku, wanda ake sa ran kammalawa nan ba da jimawa ba.

Kakakin shiyyar Kano na hukumar kula da gidajen gyaran hali da aka fi sani da gidajen yari ta Najeriya DSP Misbahu Lawan Kofar Nasarawa ya yi tsokaci kan matakan doka na rage cunkoson daurarru.

Hakan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya biya basussu da tara ga wasu daurarru su 38 dake gidajen gyaran hali na Kurmawa da Goron Dutse a Kano, jimlar kudi kusan miliyan 22.

Ko a kwanakin baya gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi amfani da hurumin da doka ta bashi wajen yin afuwa ga wasu daurarru masu kananan laifuka, kamar yadda babban jojin Kano kanyi amfani da tasa damar ya yi irin wannan afuwa ga dauarrun daga lokaci zuwa lokaci.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari:

An Zartar Da Wata Doka Da Za Ta Rage Cunkoso A Gudajen Gyara Hali Na Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG