Wakilinmu a London Sani Dauda ya ce saidai kuma a yayin da ake shirye shiryen wasan kwaikwayo da muhawarori kan makomar Bakar fata a Burtaniya, wani sashin kuma na korafi ne da cewa batun rayuwar Bakar fata a Burtaniya ba ta sake zani ba.
Bukukuwan da bana sun mai da hankali ne kan matsayin Burtaniya game da cinikin bayi da mulkin mallaka.
Esther Stanford Xosei ta kungiyar neman diyya daga Burtaniya kan laifukan cinikin bayi da mulkin mallaka ta ce “A dunkule dai biyan diyya na nuna gyara da yin sulhu da kuma maido da mutuncin al’ummar da tarihi ya nuna an gallaza masu ta wajen nuna rashin imani.