Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara Tayi Mummunar Barna


Gobara ta kona kimanin motoci ashirin da machina na haya watau okada guda hudu, a unguwar Festac dake karamar hukumar Amuwo Odofin a jihar Legas a tarayyar Najeriya.

Lamarin ya afku ne sanadiyar faduwar da wata motar daukar mai tayi a lokacin da motar ta gangaro baya ta hau gadar da ta raba unguwar Festac da Mile 2.

Wani wanda aka yi abin a kan idon sa Mr. Olufemi Popoola, ya fadawa jaridar Punch cewa faduwar motar ke da wuya sai tayi bindiga, abinda yayi sanadiyar gobarar.

Masu kashi gobara da jama’a sunyi iya iyawarsu amma sai da gobarar tayi mummunar barna, ta inda ta kone kayayyakin da ake saydawa a bakin titi da suka hada da kujeru da jakunkuna da kuma wasu motocin a wani wurin sayarda motoci da yake wurin.

Kakakin hukumar na jihar Legas Chike Oti, ya tabbatar da afkuwa hadarin da alkawari bada Karin bayani aka wadanda suka samu raunuka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG