Wata kotun tarayya dake jihar Legas, a tarayyar Najeriya, ta yankewa wani dan kasar Cote d’Ivoire mazaunin Najeriya,mai suna Grou Bi Clauvis wanda kuma aka fi sani ds Umeme Fabian Lotachukwu daurin shekaru goma a gidan kaso bisa laidfin da aka kama shi dashi na harkar mugayen kwayoyi mai suna metamphetamine dangin hodar ibilis, mai nauyin kilo 1.205.
Mai shari’ar Mojisola Olatoregun ta yanke mishi hukuncin ne bayan ya amsa laifin sa da hukumaar yaki da safarar muggan kwayoyi watau NDLEA ta kamashi dashi.
Hukumar ta kamashi ne a ranar 27, ga watan Maris a filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Legas a lokacin da ake chaje fasinjojin jirgin Qatar wanda zai tafi Doha.
Laifin a cewar mai gabatar da kara Mr. Abu Ibrahim sun sabawa sashi na 11(b) na kundin dokar Najeriya na shekarara 2004.
Lauya mai kare wanda ake karar Mr. Prosper Ojakovo ya roki kotu da tayi wa mai laifin sassauci domin shine lokaci na farko da ya taba irin wannan laifin kuma yayi alkawarin bazai sake aikata hakan ba. amma mai sharia’r tayi kira ga mai gabatar da kara da ya dubi lamarin .
Mai shari’ar tace bayan nazari “nayi duba ga cewa wannan ne karo na farko da ya aikata laifin kuma matashi ne , kuma ina sane da sashi nan 11 na tsarin dokar hukumar yaki da muyagun kwayoyi wanda dole ne, amman zan canja, kowa yasan cewa gidajen yari a cike suke, kuma mai laifin matashi ne, don haka an yanke mishi hukuncin shekaru goma a gidan yari kokuma tarar Naira milyan 10”.
Facebook Forum