Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Hallaka Akalla Mutane 80 A Rikicin Kudancin Sudan - MDD


A yau Alhamis Majalisar Dinkin Duniya ta  yi gargadin cewar jihohi 2 a kudancin Sudan “na gab da afkawa cikin bala’i” bayan da rahotanni suka bayyana cewar barkewar sabon rikici a daya daga cikin biranensu ya hallaka akalla mutane 80.

Sabon fadan ya barke ne a makon daya gabata a jihohin Kordofan ta Kudu da Blue Nile tsakanin dakarun sojin kasar da wani tsagi na kungiyar SPLM-N, mai fafutukar neman ‘yancin al’ummar Sudan karkashin jagorancin Abdel Aziz Al-Hilu.

Jami’in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai a Sudan Clementine Nkweta-Salami yace an ba da rahotan cewa fada ya lakume akalla rayuka 60 a babban birnin jihar Kordofan ta Kudu Kadugli kadai.

Rundunar sojin Sudan da babbar abokiyar hamayyarta, RSF, sun jima suna gwabza yaki akan iko da kasar tun cikin watan Afrilun 2023, inda suka haddasa matsalar jin kai mai fadin gaske.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG