Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Kaddamar Da Jirage Biyu Don Yaki Da Masu Tada Kayar Baya


Kashim Shettima a yayin kadamar da sabbin jiragen yaki
Kashim Shettima a yayin kadamar da sabbin jiragen yaki

A cewar Mataimakn Shugaban Najeriyar kaddamar da jiragen na cikin kudurorin gwamnatin tarayya na yakar matsalar tsaron dake addabar kasar.

Gwamnatin Tarayya ta jaddada aniyar magance matsalar tsaron dake addabar sassan Najeriya ta hanyar karfafa rundunonin yaki da masu tada kayar baya.

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da jirgi mai saukar ungulu samfurin “ti29 atak combat helicopter da kuma wani samfurin “beecraft king air 360er”, a sansanin sojin sama a Makurdi, babban birnin jihar Binuwe tare da wani jirgin dakon kaya da zai taimaka wajen karfafa ayyukan rundunar ta sama a kokarinta na fatattakar ‘yan ta’adda.

Mataimakin Shugaban Kasar ya samu jinjina daga jama’a a yayin da yake kaddamar da jirgin yaki samfurin “T129 atak helicopter”, inda aka gudanar da atisayen gwajin yadda yake aiki da kuma saukin sarrafarwarsa a cikin iska.

Daya daga cikin sabbin jiragen da Kashim Shettima ya kaddamar
Daya daga cikin sabbin jiragen da Kashim Shettima ya kaddamar

Gwamnan Jihar Binuwe, Hyacinth Alia, ya yabbawa gwamnatin tarayya tare da bayyana fatan samun karin kaimi a yakin da take yi da muggan laifuffuka da ta’addanci.

Kashim Shettima a cikin jirgin yaki da ya kaddamar
Kashim Shettima a cikin jirgin yaki da ya kaddamar

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Tajuddeen Abbas, ne ya jagoranci mambobin majalisar wajen bikin kaddamar da jiragen a wani mataki na nuna goyon baya.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG