Ministan ya bayyana cewa, zazzabin cizon sauro wata babbar kalubala ce a kasar, ya kuma ce zazzabin cizon sauro shine sanadin mutuwar kashi talatin bisa dari na kannan yara, abinda ke kawo koma baya ga tattalin arzikin kasar.
Binciken da aka gudanar a shekara ta dubu biyu da goma ya nuna cewa, kimanin kashi 52% na kananan yara tsakanin watanni shida zuwa biyar na haihuwa ya nuna cewa, suna dauke da kwayar cutar zazzabin cizon sauro. Kwararru sun bayyana cewa, ko da wadannan yaran sun rayu, wannan yana kawo koma baya a rayuwarsu. Cutar zazzabin cizon sauro hadi da rashin abinci mai gina jiki da zasu taimaki kananan yara su yi gima yadda ya kamata suna da hadari ga yaran.
A shekarar dubu da dari tara da hamsin da biyar ne Hukumar lafiya ta duniya ta ayyana a matsayin shekarar da zata shawo kan zazzabin cizon sauro. Sai dai har yanzu zazzabin cizon sauron yana iya kara bazuwa a kasashe da dama na duniya sakamakon canjin yanayi da ake fuskanta da zai iya bada dama ga sauron dake yada zazzabin cizon sauro.
Kwararru sun bayyana cewa, idan ana so a shawo kan yaduwar zazzabin cizon sauro a Najeriya dole ne a sami hadin kai tsakanin gwamnatocin jihohi da kananan hukumi da kuma al’umma wadanda suke bukatar hakinsu na tsabtace muhalli da kuma daukar dukan matakan kare mata masu ciki da kuma kananan yara daga kamuwa daga zazzabin cizon sauron.
Kwararru sun ce share magudanun ruwa da kuma kawar da taruwar ruwa da sauro zai haihu yana da amfani a yaki da zazzabin cizon sauro.