Rahoton ya kuma bayyana cewa, kimanin mutane miliyan biyu suna mutuwa kowacce shekara daga kamuwa da cututuka da suka kamu da su saboda shakar hayaki mai guba, an kuma fi samun yawan irin masu mutuwa da wadannan cututuka a Afrika.
Kwararru sun bada shawara cewa, bai kamata a yi watsi da irin wannan hadarin ba, suka ce ya kamata a dauke shi da muhimmanci kamar yadda ake daukar yaki da cututuka kamar tarin fuka da zazzabin cizon sauro da kuma cutar kanjamau.
Binciken ya nuna cewa yawan mutanen dake girki da itace ya shige miliyan uku, bisa ga binciken, kimanin rabin gidaje suna amfani da itace wajen dafa abinci.
Jakaden Amurka a Najeriya Terence McCulley ya bayyana cewa, gwamnatin Amurka zata bada gudummuwar dala 105 cikin shekaru biyar domin samar da murhun girki marar guba.