Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dakile Wani Hari a Birnin Abuja


Hukumar 'yan sandan farin kaya a Najeriya ko DSS ce ta sanar da dakile kokarin da wasu 'yan ta'adDa suka yi wajen kai hare-hare kan ofisoshin jakadancin Amurka da Biritaniya da wasu kadarorin kasashen yammacin Turai.

A halin yanzu kuma, jami’an tsaron Najeriya DSS sun ce sun wargaza wani shirin kai farmaki akan ofisoshin jakadancin Amurka da na Burtaniyya da ‘yan Boko Haram suka yi shirin kaiwa babban birnin tarayya Abuja.

Hukumar tsaron Najeriya ta DSS ta ce ta kama ‘yan Boko Haram dake kuma da alaka da kungiyar ISIS su biyar karshen watan jiya ne.

Mutanen da suka shiga hannun hukumar sun hada da Isa Jibril, Jibril Jibril, Abu Omale Jibril, Halidu Sule da Amhodu Salifu.

Nan take dai ofisoshin jakadancin basu maida murtani ba.

Muna da karin bayani nan gaba.

.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG