Babu alamun bukatar Majalisar Wakilai na neman babban Sufeton 'Yan Sanda ya nemi gafarar Gwamnan jihar Benue bisa kalamun da wani jami'in 'yan sandan ya yi zai yiwu. Kalamun kaskanci da aka ce wani kakakin 'yan sanda Mashood Jimoh yayi, ya fito ne bayan da Gwamnan Benue din yayi kira da cewa babban Sufeton 'Yan Sandan ya yi murabus daga mukaminsa.
A wani shirin tashar talibijan ta Channel, muhawara ta yi zafi tsakanin kakakin 'yan sanda Moshood Jimoh da kakakin Gwamnan Benue Mr. Akase inda suka dinga jefawa junansu kalamai masu tada hankali. Moshood Jimoh yace sai dai gwamnan ya yi murabus domin tamkar wanda ruwa ya ci ne a halin da yake ciki yanzu.
Sai dai babban Sufeton Ibrahim Idris ya sha nanata cewa rundunarsa na aiki tukuru domin kwantar da rigima babu nuna banbanci da bangaranci ko kabilanci ko maganar addini. Ganin yadda abubuwa ke ci gaba da tabarbarewa ya sa wasu 'yan siyasa suka marawa matakan Shugaban Kasa baya domin samun masalaha.
Sakataren jam'yyar UPN Abubakar Abdullahi Sokoto yace jimilarsu na jam'iyyu 31 sun yi nazari akan al'amuran dake faruwa sun gane cewa wasu 'yan siyasa basu karanci yanayin kasar ba. Ya kara da cewa, ana kashe-kashen mutane amma shugabanci kawai aka sa a gaba maimakon abin da zai kawo zaman lafiya har kasar ta ci gaba.
Nasiru Adamu El-Hikaya na da karin bayani a cikin rahotonsa cikin murya.
Facebook Forum