Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gargadi Dakarun Iraqi Su Kwato Ramadi daga Hannun Kungiyar ISIS


Mayakan sa akai na Sunni dake marawa dakarun Iraqi baya wajen kwato birnin Ramadi
Mayakan sa akai na Sunni dake marawa dakarun Iraqi baya wajen kwato birnin Ramadi

An gayawa dakarun Iraki cewa lokaci yayi da zasu yi kukan kura su kwaci garin Ramadi daga hanun kungiyar ISIS.

Dakarun kasar sun yiwa helkwtar lardin Anbar din kusan zobe, domin sun danna zuwa kan Birnin. Yanzu saura kilomita 15 su shiga Ramadi, bayan da suka shafe lokaci mai tsawo suna fafatawa saboda tsananin zafi, da azumin watan Ramadan, da kuma aikin Hajji.

Kakakin rundunar taron dangi da Amurka take yiwa jagoranci da take fafatawa da 'yan binidgar kanal Steve Warren ya gayawa manema alabarai haka jiya Talata ta bidiyo kai tsaye daga Bagadaza.

Wannan kiran da kuma dannawar da dakarun suke yi yana zuwa ne a dai dai lokacinda rundunar taron dangin ta zafafa kai hare hare da jiragen yaki a ciki da kewayen Ramadi cikin kwanaki 10 da suka wuce. Amurkan tace ta kai hare hare har sau 52 a yankin.

Sojojin Iraqi sun kewaye birnin Ramadi, sun kama duka kofofi huduna shiga birnin.Kanal Warren yace yanzu abunda ya rage musu shine shiga sannu ahankali cikin wurare da suke da cunkuson jama'a.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG