Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alkaluman COVID-19 a Amurka Sun Zarta Wanda Ake Fitarwa - CDC


Tambarin CDC
Tambarin CDC

Yayin da Amurka ke da kusan mutum miliyan hudu masu fama da COVID-19, bayanai daga cibiyar kare yaduwar cututtuka ta Amurka CDC ta fitar na nuni da cewa hakikanin yawan mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a wasu yankunan Amurka ya ninka har sau biyu ko ma zuwa sau 24.

Hakan na nufin cewa masu cutar a kasar ya zarta yawan alkaluman da aka fitar a hukumance.

A bayanan da ta fitar, Cibiyar CDC ta ce ta yi amfani da sanfur din jinin mutane da aka karba wadanda aka yi wa gwaji a fadin yankunan Amurka 10.

Daga cikinsu akwai na birnin New York da kudancin Florida da Missouri da kuma jihohin yammacin kasar da suka hada da Utah da Washington.

Daraktan CDC, Robert Redfield
Daraktan CDC, Robert Redfield

A Missouri, yawan wadanda suka kamu ya haura yawan wanda aka fitar har sau 13, yayin da a Utah, yawan wadanda suka kamu ya haura har sau biyu a cewar CDC.

Wadanda suka gudanar da wannan bincike, wanda aka wallafa a shafin mujallar magunguna ta JAMA, sun ce yawancin wasu mutanen da suka kamu da cutar ba su je asibiti don neman kulawa ba, domin ba sa jin alamun cutar ko kuma sukan dan ji alamunta ne kawai.

Haka kuma ana fargabar suna yada cutar ga sauran mutane.

Akalla kashi 40 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar ba sa jin alamomin wannan cuta wacce ta kashe mutum 160,000 a duk fadin Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG