WASHINGTON, D.C - Hakan shine na baya-bayan nan a cikin jerin matsanancin canjin yanayi wanda ke da tsoratarwa, sai dai yanayin bai ba masana kimiyya mamaki ba.
Matsanancin zafin na duniya ya kai maki 62.9 na Fahrenheit (digiri 17.18 Celsius) a ranar Talata, bisa ga binciken cibiyar nazarin yanayi ta Jami'ar Maine. A ranar Litinin, matsanancin zafin ya kai maki 62.6 na Fahrenheit (digiri 17.01 Celsius), wanda ya kafa tarihin da ya dauki tsawon sa’oi 24 kacal.
Wannan irin zafi mai tarihi wata shaida ce ga wadanda dama ke cewa dumamar yanayi na kara tura mu cikin makoma mai zafi, "in ji masanin kimiyyar yanayi na Jami'ar Stanford Chris Field, wanda ba ya cikin masu lissafin.
A ranar Laraba, Amurkawa miliyan 38 ne suka tsunduma cikin wani nau'in zafi da aka yi shekarsa, in ji babban jami’ar kimiya Sarah Kapnick.
Ta ce zafi a duniya ya samo asali ne daga dumamar yanayi na El Nino ta tekun Pasifik wanda ke kara zafi a duniya yayin da yake sauya yanayin na duniya, banda sauyin yanayi da mutane ke haddasawa ta wajen girki da itace, da amfani da mai da kuma iskar gas.
-AP