Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Hasashen Wanda Trump Zai Zaba Ya Maye Gurbin Ginsberg a Kotun Koli


A jiya Litinin shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya rage yawan sunayen mutanen da yake so ya zaba alkalin kotun koli zuwa mutum biyar, kana ana sa ran zai sanar da wanda zai maye gurbin marigayiya Mai shari’a Ruth Bader Ginsburg a ranar Juma’a ko Asabar.

Trump ya ce zai zabi mace kana ya bayyana sunayen matan da suka hada da Amy Coney Barret da Barbara Lagoa da kuma Allison Jones Rushing, ‘yan ra’ayin rikau da ya nada su zuwa kotunan tarayya na daukaka kara a cikin ‘yan shekarun nan.

Sai dai yaki bayyana sunaye sauran mata biyun da ke cikin wadanda ya zaba, yayin wata hira mai tsawo da ya yi a kan shirin Fox & Friends, na telbijin din Fox.

Trump ya ce zai yi sanarwar wanda zai maye gurbinta ne bayan an kamala addu’o’in jana’izar Ginsburg fitatcciyar ‘yar sassaucin ra’ayi mai shekaru 87 da ta rasu a ranar Juma’a da ta gabata bayan fama da tayi da cutar sankara.

A ‘yan shekarun nan Shugaban Amurka Donald Trump ya nada Amy Coney Barrett, da Barbara Lagoa da Allison Jones Rusing, masu ra’ayin rikau a matsayin alkalan kotun daukaka kara, kuma ana sa ran a yanzu zai iya daukan daya daga cikin su ya sa a matsayin wanda zai haye kujerar dindindin a kotun kolin.

Da alama kuma suna kan gaba a jerin sunayen na zabin shugaban Amurka domin maye gurbin Mai Shara’a Ruth Bader Ginsburg, mai sassaucin ra’ayi wadda ta rike mukamin na tsawon shekaru 27 kafin mutuwarta ranar Juma’a, wata daya da rabi kafin zaben 3 ga watan Nuwamba, inda za’a kara tsakanin Trump da Biden.

Kowace daya daga cikin matan uku, Barrett mai shekaru 48 da Lagoa mai shekaru 52 da Rushing mai shekaru 38 na iya samun goyon baya kai tsaye na ‘yan majalisar dattawa na jam’iyyar ripublican a majalisar dattawa mai rinjayen ‘yan republican. Haka kuma ko wacce daga cikin su na iya fuskantar adawa daga ‘yan democrats.

Da yawa daga cikin ‘yan Democrats na iya kin amincewa da tabbatar da ko wace daya daga cikinsu saboda zai iya kara rinjayen masu ra’ayin majan jiya 6 da 3 daga 5 da 4 kuma zai iya sahafar shawarwari akan batutuwa da dama, ciki har da batun zubar da ciki, bakin haure, harkar lafiya ‘yancin addini da dai sauransu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG