Tun a ranar Talatar da ta gabata ne bangarorin siyasar kasar ta Nijar suka fara fuskantar juna da zimmar tattauna hanyoyin kawo karshen ka-ce-na-cen da ke tsakanin su yau kusan shekaru biyu.
Lura da alamun yiyuwar samun fahimta ya sa wadanan ‘yan siyasa a karksahin shugabancin Firaminista Birgi Rafini kiran taron manema labarai a yammacin jiya Laraba domin yi wa jama’a bayani kan wannan yunkuri.
Tsohon Firaminista Shehu Amadou na kawancen jam’iyyu masu mulki, ya yi kira ga ‘yan adawa da su zo su yi aiki tare domin su fuskanci irin tarin matsalolin da ke damun kasarsu.
‘Yan adawa wadanda suka kauracewa dukkan wani zaman da ya shafi tsare- tsaren zabukan da ke tafe sun gindaya wasu sharudda a matsayin wani matakin share fagen soma tattaunawar.
Sai dai mataimakin shugaban kawancen ‘yan adawa na FRDDR, Amadou Djibo Max, ya ce suna bukatar karin shaidu da za su zo daga kasar wajen domin shaida irin yarjejeniyar da za su rattaba hannu akai.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma daga Yamai:
Facebook Forum