An fara kidaya kuri'u a kasar Ivory Coast ko Cote D'Ivoire, a bayan zaben fitar da gwani na shugaban kasa da ya haddasa zub da jini kafin ranar zabe, da kuma zarge-zargen cin zarafi ranar zaben daga dukkan sassan biyu.
Wani kakakin shugaba Laurent Gbagbo yace ba a gudanar da zaben tsakani da Allah ba a yankunan arewacin kasar inda abokin hamayyarsa Alassane Ouattara yake da karfi da goyon baya.
Shi kuma manajan kyamfe na Mr. Ouattara, Marcel Tanon, yayi zargin cewa masu jefa kuri'a da yawa sun kasa isa rumfunan zabe jiya lahadi a saoda yadda magoya bayan shugaba Gbagbo suka rika tare su, su na hana su kaiwa ga wuraren jefa kuri'un nasu.
Shugaban tawagar 'yan kallo ta Tarayyar Turai, Cristian Preda, ya ce lallai an ga shingaye a wurare da dama inda ake hana magoya bayan Mr. Ouattara da na Mr. gbagbo kaiwa ga rumfunan zabe.
Miliyoyin 'yan kasar ta Cote D'Ivoire sun kada kuri'unsu jiya lahadi a wannan zaben da aka shirya domin sake hade kasar wadda yakin basasa na 2002 ya raba.