Tsohon Firayim ministan kasar Ivory Coast ya samu goyon bayan da ka iya zamowa mai matukar muhimmanci a zaben fitar da gwani na shugaban kasa da zai kara da shugaba Laurent Gbagbo nan gaba cikin watan nan.
Jiya lahadi, tsohon shugaba Henri Konan Bedie yayi kira ga magoya bayansa da su jefa kuri’unsu ma Alassane Ouattara a zaben fitar da gwanin na ranar 21 ga watan nan na Nuwamba. Mr. Bedie shi ya zo na uku a zagayen farko na zaben shugaban kasar da aka ranar lahadi ta sama, inda ya samu kashi 25 cikin 100 na kuri’un da aka jefa.
Shugaba Gbagbo, wanda ya samu kashi 38 cikin 100, da Ouattara, wanda ya samu kashi 32 cikin 100, sun haye za su gwabza a zagaye na biyun. Tun kafin wannan zaben, Mr. Bedie da Mr. Ouattara sun yi alkawarin zasu goyi bayan kowane daya daga cikinsu idan ya haye zai fuskanci shugaba Gbagbo a zagaye na biyu.
Zaben da aka yi a ranar lahadi ta sama shi ne zaben shugaban kasa na farko tun yakin basasar shekarar 2002.
Wa’adin shugaba Gbagbo a kan mulki ya kare tun shekarar 2005, amma an sha jinkirta gudanar da zabe a saboda kasa karbe makaman ‘yan tawaye da kuma gardama a kan wadanda suka cancanci jefa kuri’a a kasar.