Dukkan ‘yan takara biyu a zaben shugaban kasa na Ivory Coast ko Cote D’Ivoire, sun yi rantsuwar fara aiki jiya asabar a yayin da kasar ta abka cikin rikicin siyasa.
An rantsar da shugaba Laurent Gbagbo a wani bukin da gidan telebijin na kasar ya nuna, a bayan da Majalisar Tsarin Mulkin Ivory Coast ta ce shi ne ya lashe zaben da kashi 51 cikin 100. Amma tun farko, hukumar zabe ta kasar ta ce shugaban hamayya Alassane Ouattara, shi ne ya lashe zaben da kashi 54 cikin 100.
Faransa da Amurka, da Tarayyar Kasashen Turai, da Tarayyar Kasashen Afirka duk sun bi sahun Majalisar Dinkin Duniya wajen amincewa da Alassane Ouattara a zaman zababben shugaban Ivory Coast, sun kuma yi kira ga Mr. Gbagbo da ya amince da wannan sakamako.
Tun da fari a jiya asabar din, shugaban majalisar zartaswar Kungiyar Tarayyar Turai, Jose Manuel barroso, ya bayyana Mr. Ouattara a zaman halaltaccen zababben shugaban Ivory Coast.
Asusun lamunin kudi na duniya, IMF, yace ba zai yi aiki da gwamnatin kasar Ivory Coast ba sai wadda Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita.
Firayim ministan Ivory Coast, Guillaume Soro, wani tsohon madugun ‘yan tawaye da ya shiga gwamnatin hadin kan kasa da Mr. Gbagbo karkashin yarjejeniyar zaman lafiya ta 2007, ya fada jiya asabar cewa Alassane Ouattara shi ne zababben shugaban kasar.
Jiya asabar, sojoji sun kafa shingaye na tare hanyoyi a kewayen Abidjan, babban birnin kasar. Da ma dai kasar tana cikin dokar hana yawo, sannan an hana dukkan kafofin yada labarai na kasashen waje watsa labaransu a kasar.
Mazauna birnin Abidjan sun bayar da rahoton jin kararrakin harbe-harbe cikin dare a sassa dabam-dabam na birnin. Jiya asabar da rana, magoya bayan Mr. Ouattara sun fito kan tituna a rana ta biyu a jere su na kona tayu tare da kafa shingaye. Mutane 14 ne suka mutu ya zuwa yanzu a tashin hankalin siyasa.