Kundin tsarin mulkin Nijer da kundin zaben kasar sun bayyana mataimakan ‘yan majalisa wato “suppleant” da Faransanci, a matsayin wakilai masu jiran gado, sai dai bayan shekaru kusan talatin na demokradiyar kasar, bayanai na nuna har yanzu ba a basu darajar da ke daidai da wannan matsayi kamar yadda suka koka a karshen wani taron da suka gudanar a birnin Yamai. .
Dokokin zaben Nijer sun tanadi cewa mataimakin dan majalisa wato “suppleant” shine ke maye gurbin dan majlisar yankin da ya fito idan aka yi katari ya gaza, ko dalilai masu nasaba da canjin wurin aiki ko kuma idan rai ya yi halinsa, sai dai alamu na nunin ‘yan siyasa na kokarin soke wannan mataki inji
Taron na tsawon wuni guda ya danka takardun shawarwarin da ya tsayar a hannun jami’an da suka wakilici gwamnati a wannan haduwa don ganin an hanzarta daukar matakan magance matsalolin sabbin zababbun wakilan al’umma da ake sa ran tantancewa a zaben ‘yan majalisa na watan Disamban 2020.
Ga wakilin muryar Amurka a Yamai Souley Moumouni Barma da cikakken rahoton:
Facebook Forum