Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Amfani Da Bokaye Don Magance Safarar 'Yan-Mata


Kamfanin dilancin labarun Reuters ya bada labarin cewa, shugaban hukumar yaki da safara mutane ta NATPIP Mrs. Julie Okah-Donli, ta dauki wani sabon mataki wajen magance matsalar safara mutane musamman ‘yan mata don zuwa kasashen turai da zummar yin karuwanci.

Shugabar hukumar ta koka da yadda ake daukar ‘yan mata da basu san hawa ba balle sauka da kwadaita musu samun abun duniya da akan yi, wajen yaudarar su don tafiya kasashen wajen, da cewar zasu samu aikin yi mai kyau.

Birnin Benin na Jihar Edo shine gari da yayi kaurin suna wajen koyarwa da kitsa duk wasu makircin shiga harkar karuwanci a kasashen turai, don haka yasa shugabar ta dauki wani sabon matakin magance wannan matsala.i, Ta shiga amfani da bokaye da zummar gano ire-iren surkullen da sukeyi wajen sauya tunanin ‘yan mata.

Hada baki da Bokayen da tayi ya taimaka matuka wajen shawo kan wannan matsalar, domin ta gano dalilai da kuma irin yaudarar dake cikin harka. Ta kara da cewar babban dalilin zuwanta shine, an yard ko kuma ana yarda da hasashen bokayen matuka musamman idan akayi maganar sa’a a harkar sana’ar karuwanci.

Fitar labarin ke da wuya sai ga labarin safarar ‘yan mata zuwa kasashen turai ya bayyana, anata kawo musu labaran hanyoyi da ake bi wajen shawo kan ‘yan matan da kuma wadanda ake tirsasawa shiga sana’ar.

Ta kara da cewar daga shekarun 2014 zuwa 2016 an samu karuwaryawaitar ‘yan mata dake fita zuwa kasashen turai don sana’ar karuwanci. Akalla an samu ‘yan mata sama da 11,000 daga Najeriya da suka kwarara zuwa kasashen turai a shekarar 2016.

Dubbai kuwa sunyi yunkurin tafiyar amma basu samu nasarar ba, bisa wasu dalilai daban daban, wanda ake kwadaita musu romon baka da cewar zasu samu aiki mai albashi na kwarai.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG