Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabuwar Wayar iPhone SE Ta Sami Karbuwa A China


Miliyoyin mutane a kasar China sun yi odar sabuwar wayar nan ta iPhone SE ta kamfanin Apple, tun ma kafin a fara sayar da ita, yayin da kamfanin ke kokarin fadada kasuwar wayarsa a wannan kasa da masu sarrafa waya na cikin gida ke fuskantar gasa sosai.

Kamfanin Apple yace wannan waya ta iPhone SE it ace mafi arha da ya taba sarrafawa, kuma wani sabon yunkuri ne na janyo hankalin masu son sayen wayar da ba ta da tsananin tsada.

Wayar ta iPhone SE ana sayar da ita a kan dala 400, kimanin Naira dubu 120, ga wadda take iya ajiye bayanai masu nauyin GVigabyte 16, yayin da mai iya ajiye bayanai na gigabyte 64 ake sayar da ita a kan dala 500 kimanin naira dubu 150.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG