Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tabarbarewar ilimi a jihar Bauchi ya kai inda hatta kujerun yara babu a makarantu


Yaran makaranta
Yaran makaranta

Ilimi a jihar Bauchi ya tabarbare inda hatta kujerun da yara zasu zauna su dauki karatu babu a kusan duk makarantun jihar haka ma akwai malamai da suka yi shekaru da dama ba'a kara masu girma ba kuma su kan yi wata da watanni ba'a biyasu albashi ba.

A cikin garin Bauchi makaranta daya ce tak yaranta ke da kujerun zama su dauki karatu amma duk sauran basu da kujeru ga kuma rashin takardu da rashin kayan aikin malamai da dai sauransu.

Kowace shekara gwamnati tana sa ilimi cikin kasafin kudinta to amma fannin ilimi ba ya cin gajiyar kudaden. Ko wannan gwamnatin ta yanzu ta ware kaso mai tsoka ma ilimi amma tana yiwuwa shekara ta kare ba'a yi komi ba.

A jihar Bauchi akwai malamin da ya yi shekaru goma sha daya ba'a kara mashi girma ba ko karin albashi. Manyan ma'aikatan gwamnati basa kai 'ya'yansu makarantun gwamnati domin basu damu dasu ba.

Gwamnati ce ta kawo tabarbarewar ilimi. Tunda aka kashe makarantun horas da malamai ba'a maye gurbinsu da wasu ba. Jami'an gwamnati su suke kawo 'yanuwansu da basu koyi ilimin koyaswa ba su sasu a matsayin malamai. Wadda bata yi karatun koyaswa ba an kawota dole ta yi malunta sai ta dagula lamarin yadda ta iya yi. Gwamnati ita ce umalubaisan wulakantar da malamai da ilimi. Idan ana son a farfado da ilimi dole ne a dawo da makarantun horas da malamai, kana a biya malamai albashinsu da duk alawus alawus da ake ba ma'aikata.

Banda laifin gwamnati da malamai akwai sakaci a bangaren iyaye. Wasu iyaye basa duba abubuwan da aka koyawa 'ya'yansu a makaranta. Idan ma ba'a koya masu komi ba ba zasu sani ba domin basa sa ido a ilimin 'ya'yansu.Idan iyaye na sa ido suna iya zuwa makarantun 'ya'yansu su yi tambayoyi su fada ma malamai abun da suka gani su kuma bukaci a sa ma yaran ido.

Yakamata iyaye su ma su tashi su taimaki makarantu da abubuwan da suke bukata saboda gwamnati ba zata iya yin duk abubuwa ba. Iyaye ma nada rawar da zasu taka. Masu arziki su duba su ga inda zasu iya taimakawa.

A bangaren gwamnati musamman ta APC tun daga kan Buhari zuwa kasa ta sha alwashin inganta ilimi a duk fadin kasa. Yanzu ne aka gabatar da kasafin kudi sai a jira a ga abun da zai faru a fannin ilimi.

Ga cikakken muhawara akan ilimi a jihar Bauch

XS
SM
MD
LG