Wasu iyaye ‘yan asalin kabilar Yarbawa, mazauna kasar Brazil, sun fuskanci wani banbanci da baza su taba mantawa da shi a rayuwar suba. Dokar kasar Brazil, itace idan aka haifi jariri za’a rubuta sunan jaririn a cikin kundin sunayen ‘yan kasa. A dai-dai lokacin da Cizinho Afreeka da matar shi Jessica Juliana, suka samu karuwar jaririya mace, sun isa ofishin da ake rajistan sunayen yara.
Amma abun mamaki a alokacin da suka fadi sunan ga ma’aikatan ofishin, sai sukace wannan sunan bai dace da wannan yarinyar ba. Dalili kuwa shine wai sunan yarbawa ne yanada wahalar fade a gare su, sunan dai shine “Makeda Foluke” ma’aikatan ofishin sunyi tsayin daka kan cewar sai dai a canza ma yarinyar suna. Iyayen sun bayyanar da sunan a matsayin sunan da suka sa mata don haka suna bukatar a saka sunata a hakan.
Ma’aikatan sun bayyana musu cewar basu so ana sama yara sunan da idan yaro ya girma zai sa ya zama mutumin banza saboda sunan shi, sun kuma iya gano cewar wannan sunan a yaren “Portuguese” na nufin “Wahala na iya samuwa nan gaba ga mutun cikin rayuwar zamantakewa” don haka baza su bari a saka ma wannan yarinyar wannan sunan ba. Kada a gaba ta zama mara jin magana.
Wannan takaddamar ta jawo hankalin mutane da dama, wanda iyayen naganin kamar hakan wata hanyace ta nuna banbanci launin fata. A bangaren ma’aikatan sunayin hakan ne don kokarin kauce ma wani mugun abu akan yarinyar idan ta girma, a dalilin sunan ta.