Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Yau PSG Zata Yi Tattaki Zuwa London Domin Karawa Da Chelsea


Yau laraba ne za a samu karin kungiyoyi guda biyu da zasu haye zuwa ga wasannin kwata fainal na cin kofin zakarun kulob kulob na Turai, bayan da a jiya talata Real Madrid ta zamo kungiyar farko da ta haye sa’ilin da ta doke AS Roma da ci 2-0, ta haye da ci 4 da babu ke nan idan aka hada da karawar farko.

Kwararrun tamaula sun ce Real Madrid ba ta burge ba a wasan na jiya.

Ita ma Wolfsburg ta haye zuwa ga wasannin kwata fainal bayan da ta doke Gent da ci 4-2 idan aka hada karawa biyun da suka yi.

A yau PSG, tattaki zata yi daga Paris zuwa London domin karawa da kungiyar Chelsea. A karawarsu ta farko a Paris, PSG ce ta doke Chelsea da ci 2-1.

Kungiyar Benfica zata yi tattaki zuwa gidan ‘yan Zenit domin ganin ko zata iya kare ci daya mai ban haushi da ta yi ma Zenit a karawarsu ta farko ranar 16 ga watan fabrairu.

Daga can Najeriya kuma, Samson Siasia yace yayi Imani ‘yan Super Eagles zasu faranta ma ‘yan Najeriya ciki a gwabzawar da zasu yi da Masar a wasan share fagen cin kofin kasashen Afirka da zasu yi a Kaduna ranar 25 ga watan nan na Maris.

Siasia yace ladabi da nuna hazaka da kwarin guiwa da kuma goyon bayan ‘yan Najeriya zasu iya sanya ‘yan Super Eagles su nuna bajimtar da suka taba nunawa a lokacin da suka doke Masar da ci 4-0 a wani wasan share fagen cin kofin duniya a shekarar 1977 a Lagos.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG