Wasu kadan daga cikin abubuwan da shaye-shaye kan iya haifarwa ga duk wani ma’abuci shan wasu kwayoyi da basu da ma’ana ga rayuwar dan’adam. Kodai don samun kuzari ko neman wasu abubuwa da dama. Baya ga lalata jiki, kwakwalwa da sukan sa ma mutun da wasu halaye na kakani kayi, shaye-shaye kan iya zama ummul haba isin koma baya ga rayuwar mutun.
Shahararriyar ‘yar wasan kwalon “Tennis” ta kasar Russia, Maria Sharapova, wadda tazama gogaggiya a wasan, tasamu lashe wasanni 5, a jere a jere, wanda hakan yasa tana daga cikin jerin ‘yan wasa masu kudi a duniya. Amma a shekarar da ta wuce ta buga wasa inda aka samu damar gano cewar ta sha wata kwaya don ta kara mata kuzari. Wanda a dalilin haka yanzu ta bayyanar da cewar lallai wannan laifin ya sata cikin tsaka mai wuya. Suma kamfanonin da ke daukar nauyin wasan da take bugawa kamar su kamfanin Nike, kamfanin agogon Swiss, da kamfanin motoci na kasar Germany Porsche, sun nisanta kansu da wannan hali da tasa kanta.
A yanzu dai wannan laifin na shaye-shayen kan iyasa ta rasa duk wani abu da ta samu a rayuwar ta. Don a yanzu haka wasu daga cikin kamfanoni sun soke kwantirakin dake tsakanin su da ita. Wannan na daya daga cikin jerin kadan daga cikin abubuwan da shaye-shaye kan iya haifarwa a rayuwar dan’adam.