Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sharuddan Shiga Najeriya Ta Jirgin Sama


'Yan Najeriya Na Dawowa Gida
'Yan Najeriya Na Dawowa Gida

Kwamitin musamman na yaki da annobar Coronavirus na gwamnatin tarayya ya fitar da ka’idojin shiga Najeriya daga kasashen waje.

Sanarwar da aka fitar ranar jumma’a 4 ga watan Satumba, dauke da sa hannun sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin Bos Mustapha, ta gabatar da matakan da matafiya da kuma hukumomi za su dauka na tabbatar da cewa masu shiga Najeriya daga kasashen ketare basu dauke da cutar CODVID-19 .

Ga ka’idojin da aka fitar daga ofishin sakataren gwamnatin tarayyar:

Shirin da matafiyi zai yi kafin ya tashi zuwa Najeriya:

Matakan kariyar da za’a dauka sun shafi dukan fasinjoji da zasu shigo ko ficewa daga Najeriya a lokacin da ake fama da annobar Coronavirus a kasashen duniya.

  • Dole ne duk fasinjojin da zasu shigo Najeriya su nuna shaidar gwaji da ya tabbatar da cewa ba sa dauke da cutar Coronavirus, wanda da aka yi daga kasar da za su fita kafin su shiga jirgi. Ya zama wajibi a yi gwajin na PCR cikin sa’o’i 96 kafin barin kasar, za’a gwammace matafiyin ya yi gwajin cikin sa’o’i 72 kafin shiga jirgi. Za’a amince da sakamakon gwajin ne kawai idan aka gudanar da shi a cibiyoyi na musamman.
  • Ba za’a amince da duk gwajin da ya wuce sa’o’i 96 da hukumomi suka tsara kafin shiga jirgi ba, kuma ba za’a bari fasinja ya shiga jirgin ba, kuma an umarci fasinjoji su kiyaye mafi karancin lokaci na sa’o’i 72 a lokacin shigan jirgin.
  • Ana bukatar duk mai niyyar yin tafiya ya yi rijista ta yanar gizon sufurin Najeriya wato Nigeria International Travel Portal – http://nitp.ncdc.gov.ng, tare da biyan kudin sake yin gwaji da zarar sun shigo Najeriya. Da zarar sun gama biya, za su sami sakon Email daga asibitin da suka zaba da za a yi masu gwajin, tare da hanyoyin da za su bi wajen yin gwajin PCR na biyu rana ta bakwai da shigowa Najeriya. Fasinjoji za su zabi cibiyar da za su bai wa samfurin gwaji da su ke so tare da lokaci, da ranar da za’a karbi samfurinsu. Za’a iya samun jerin sunayen cibiyoyin gwajin PCR dake fadin Najeriya a shafin yanar gizon da aka kirkiro saboda yin rijista tare da shafin yanar gizon hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa da za’a biya kudin gwajin .
  • Za’a bukaci fasinjoji su cika takardar shaida/bayani ta yanar gizo dake shafin yanar gizon tafiye-tafiyen kasa da kasa na Najeriya. Za’a bukaci a mika kwafin takardar da suka cika ta yanar gizo lokacin da suka sauka a kasar. Za su kuma tabbatar da cewa sun ba da sahihan bayanai kamar lambobin wayar tarho da adireshi a takardar da suka cika, kuma ya zama wajibi lambobin wayar tarhon matafiyan su kasance suna aiki. Ya zama wajibi fasinjoji su fadawa ma’aikatan lafiya a filin tashi da saukar jiragen sama da suka sauka, bayan cika bayanan yanayin lafiyarsu a takardar da gwamnati ta samar, da duk wani sauyin da suka fuskanta.
  • Gabanin shigan jirgi, ana bukatar fasinjoji su wallafa sakamakon gwajin PCR din su na annobar Coronavirus a shafin yanar gizon gwamnati tare da kawo shaida ta na’ura ko kuma sakamakon na zahiri a filin tashi da saukar jiragen sama. A lokacin shiga jirgi, ana bukatar duk fasinjoji su fuskanci gwajin duba yanayin zafin jikinsu da amsa tambayoyi game da alamun cutar Coronavirus, hukumomi ba za su bar duk fasinja mai alamar cutar Coronavirus ya shiga jirgi ba.
  • Ana bukatar dukan kamfanonin jiragen sama su dauki fasinjojin da ke da sakamakon da ya nuna ba sa dauke da cutar korona da aka yi cikin sa’o’i 96 kawai kafin shiga jirgin. Za’a hukunta duk kamfanin jirgin sama da ya dauki fasinjan da ba shi da takardar shaidar cewa ba ya dauke da cutar Coronavirus na PCR ko kuma sakamakon gwajin da ya shafe sama da sa’o’i 96 kafin shiga jirgi, bisa wannan tsarin: (a) Ba za’a bar duk fasinjan da ba dan Najeriya ba ya sauka a kasar tare da mayar da shi kasar da ya fito wanda kamfanin jirgin zai dauki nauyin biya. (b) Za’a bar ‘yan Najeriya su shiga, sai dai hukumomi za su killace su bisa ka’ida na tsawon kwanaki 8 zuwa 14 (bisa la’akari da sakamakon gwajin PCR din su da za’a gudanar bayan kwanaki 7 da shigowa kasar) a cibiyoyin gwaji da kula da masu dauke da Coronavirus da gwamnatin ta amince da su tare da daukar nauyin fasinja. (c) Gwamnati za ta ci tarar duk kamfanin jirgin saman da ya saba ka’ida har dala dubu uku da dari biyar ($3,500) kan kowane fasinja da ba a ga sakamakon gwajin sa ba saboda rashin bin ka’idojin shiga jirgi da gwamnati ta gindaya.
  • Da zarar shigowa Najeriya

Za’a bukaci duk fasinjojin da zasu shigo Najeriya da:

(i). Su bi tsarin duba su a sashin bincike na filin tashi da saukar jiragen sama tare da nuna shaidar yanar gizo ko na zahiri na sakamakon gwajin PCR da suka yi kafin shiga jirgi da shaidar biyan kudin da za’a sake yi musu gwaji na biyu a Najeriya.

ii. Za su mika fasfo din su don tantancewa ga ma’aikatan kula da shige da fice na Najeriya. Za’a turawa dukan cibiyoyin karba da gwajin samfurin PCR na Najeriya shafin fasfo na bayanan duk fasinjoji da ke dauke da hotonsu domin tantance su yadda ya kamata kafin a karbi samfurinsu. Hukumar kula da shige da ficen Najeriya ba zata rike fasfo din fasinja ba.

iii. Za su killace kan su na tsawon kwanaki 7 a lokacin da dole su kaucewa cudanya da abokai, yan’uwa, abokan aiki, da sauran al’umma (kamar ba da tazara). Kada fasinjoji su manta, su rinka duba sakon Email din su a kai-a-kai saboda karin bayani a kan shirin kara yin gwajin PCR na Coronavirus daga duk cibiyar da suka zaba.

iv. Su kai kan su a cibiyoyin karbar samfuri a kwanaki bakwai da isowar su Najeriya; za’a karbi samfurin su tare da gudanar da gwajin PCR kuma akwai yiyuwar cibiyoyin gwajin za su turawa fasinjoji sakon tuni, kwana daya kafin ranar da za a yi gwajin. Ka lura da haka:

(a) Za’a yi wa duk fasinjan da ya ki bayyana a cibiyar karbar samfuri bayan kwanaki bakwai da shigowa Najeriya sakon tuni ta wayar tarho tare da tura bayanan su ga tawagar binciken lafiyar jama’a da hukumar NCDC domin bibiyar su.

(b) Za’a bukaci cibiyoyin karbar samfuri masu zaman kansu su ba da bayanan fasinjoji da su ka ki barin a sake yi ma su gwaji bayan kwanaki 14 domin hukunta su. Za’a iya dakatar da amfani da fasfo din fasinjan ko kuma a saka sunan sa a jerin sunayen mutanen da za’a sanya wa ido na tsawon watanni 6 tare da hana su tafiya kasashen waje na tsawon watanni 6.

(c) Za’a fitar da sakamakon gwajin cikin sa’o’i 24 zuwa 48 kuma za’a bai wa tawagar kula da lafiyar jama’a da hukumar NCDC rahoto a kan sakamakon fasinjojin.

(d) Za’a kula da duk fasinjan da sakamakonsa ya nuna yana dauke da korona kamar yadda ka’idojin kula da masu dauke da cutar na Najeriya ya tanadar.

(e). Duk fasinjan da sakamakon sa ya nuna ba ya dauke da cutar zai daina killace kai a kwana na 8.

(f) Ba za’a bar duk matafiyin da ya kai rahoto ko kuma ya fara samun alamomin cutar Coronavirus a lokacin da ya shigo Najeriya ko lokacin da ake tsakar tantance shi ya killace kan shi ba, gwamnati ce za ta killace shi bisa ka’ida.

(g) Ga duk wandanda aka koro daga wata kasa, idan sakamako ya nuna mutum daya na dauke da cutar Coronavirus, za’a bukaci a yi karin tantancewa ga duk wanda ke kusa da shi tare da kara gudanar da gwajin PCR a kan su idan bukatar hakan ya taso.

(h) Ma’aikacin tawagar kula da lafiyar jama’a zai sa wa fasinja ido a lokacin da ya killace kan sa. Saboda haka, za’a bukaci fasinja ya ba da lambar waya da ke aiki a kan takardar da suka cika ta yanar gizo. Za’a yi wa duk wanda ya ji alamar cutar Korona a lokacin da ya ke killace gwaji nan take. Idan ya kamu da cutar, za’a kula da shi kamar yadda ka’idojin kula da masu dauke da cutar Coronavirus na kasar suka tanadar.

Fita daga killace kai

Za a bar duk fasinja da ba’a sami yana dauke da cutar Coronavirus ba bayan kwanaki 7 na killace kai, ya fita a rana ta 8.

Wadanan ka’idoji zasu fara aiki a ranar asabar 5 ga watan satumbar shekarar 2020.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG