Za a iya karbar shi ne a ofishin jakadancin Najeriya a kasashen, wanda zai maye gurbin takardar da ake bayarwa ga 'yan kasar da ke bukatar tafiya, amma ba tare da sanin inda ainihin fasfo din su yake ba.
Karin bayani akan: Muhammad Babandede, Ogbeni Rauf Aregbesola, Nigeria, da Najeriya.
Duk wani dan kasar da ya batar da fasfo din shi, kuma yake da bukatar tafiya zuwa Najeriya, zai iya zuwa ofishin Najeriya da ke kasar da yake, zai biya kudin karbar fasfo din, wanda za a ba shi fasfo mai shafi hudu, wanda aikin shi kadai ya shigar da mutum kasar, daga bisani sai ya nemi fasfo na dindindin.
A jiya Talata Ministan harkokin cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola, ya kaddamar da shirin a shelkwatar hukumar shige da fice ta Najeriya. Fasfo din na wucin gadi yana aiki na tsawon kwanaki 30 daga ranar da aka buga shi.
Shugaban hukumar shige da fice ta Najeriya, Muhammad Babandede, ya ce shi dai fasfo din an fito da shi ne don ya maye gurbin takardar da akan bai wa 'yan kasar da ke kasashen ketare kuma suka batar da nasu fasfo din, da kuma kara bada kariya ga harkar shige da fice cikin kasar.