A jamhuriyar Nijer masu tsara bukin baje kolin madimkan nahiyar Afrika ( FIMA) da ya kamata a soma a gobe laraba a birnin Yamai, sun bada sanarwar dage wannan buki zuwa wata ranar da ba a bayyana ba saboda dalilan tsaro.
Harin ta’addancin da aka akai a makon jiya a birnin Bamako na kasar Mali da wadanda aka kai makon da ya gabata a birnin Paris na kasar Faransa wadanda suka haddasa asarar rayukan mutane da dama sune dalilan da suka sa hukumomin Nijer dage festival din na FIMA karo na 10.
Fitaccen madimkin nan na kasar Nijer bugU da kari jagoran bukin wato shine ya bayyana hakan a taron manema labaran da ya kira a yammacin talata .
Yace tuni baki sama da 40 suka iso Nijer domin halartar wannan faestival. cikin dare kuma ana sa ran isowar wasu fiye da 50 sannan wasu mutane sama da 100 zasu shigo a washe gari.
Gwamnatin kasar tace ta dage wannan buki domin taya makwafta juyayin abinda ya same su, sannan tace matakin zai taimaka a kara karfafa kwanciyar hankali saboda haka wajibi ne A bada hadin kai.
Bakin da suka shigo gari daga kasashen duniya daban daban domin halartar wannan buki na FIMA sun bayyana matukar kaduwa da jin labarin matakin dage wannan baje koli na kasa da kasa.
Marc Richet, wani dan kasar faransa mai sana’ar daukar hoto ya ce "na bukin fima wata hanya ce ta sanarda duniya irin dimbin albarkatu da al’adun nahiyar Afrika saboda haka nazo in kara kusantar madimkan wannan nahiyar wadanda a yau suke gogayya da sharararun madimkan faransa irin su YVES SAINT LAURENT su CHRISTIAN DIOR da su PASCAL GAUTIER sai dai kash bukin ya sha ruwa jiki ya mutu kwata kwata buki".
Ranar 25 ga wannan watan ne ya kamata a soma wannan buki sai dai a maimakon jawabin kaddamarwa gwamnatin Nijer ta hanyar kakakinta za ta sanarda jama’a matakin dage festival din a hukunce a matsayin hanyar bada hakuri ga mutanen da matakin ya cutawa.
Ga rahoton wakilin muryar amurka daga Yamai Sule Mumini Barma.