Yayin da adadin marayu sai karuwa ya ke yi sakamakom iyayen yara da Boko Haram suka kashe a arewa maso gabashin Najriya. Wata yarinya ‘yar shekara goma sha hudu ta bi sawun kungiyoyin sa kai ta hanyar wallafa littafi wanda ta yi wa lakabi da jimamin marayu (wato stigma of recognition) da niyyar kafa jidauniyar da zata rika tallafawa marayu.
Littafin mai shafi saba'in, jigon sa shine irin halin kewa da kadaici da marayun ke fuskanta, marubuciyar ta rasa iyayenta ne tun tana 'yar karama.
A hirar da wakilin sashin Hausa na muryar Amurka yayi da ita, ta bayyana cewar tana da ra'ayin taimakwa marayu irin ta, ta hanyar neman kudi domin ta sayi abinci da sutura da sauran su ta rika zagayawa tana rabawa marayu a duk inda suke a fadin jahar ta Adamawa.
Mawallafiyar littafin, A’isha Bukar Kiri daliba ce, ‘yar aji uku a makarantar sakandare ta barikin sojoji da ke Yola, ta ce jigon littafin shine irin halin zaman kewa da kadaici da marayu ke fuskanta wanda ta gina akan irin halin da ta sami kan ta a ciki lokacin da iyayenta suka rasu tun tana karama.
Wakilinmu da ke Yola Sanusi Adamu na dauke da rahoton.