Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cin Zarafin Mata


Cin zarafin iyali rikici ne dake faruwa tsakanin ma'aurata a gidanjen su wanda ya hada da duka ko raunata daya daga cikinsu, fyade tsoraratarwa da sauransu.

Majalisar dinkin duniya tace daga cikin uku na mata a duk duniya na fama da matsalar cin zarafi a gida.

Shi dai cin zarafin nan an fi samunsa tsakanin ma'aurata ko wadanda suka shaku inda kimanin mata miliyan 603 ke fama dashi.

A gida Nijeriya kuwa yara da mata wadanda shekarunsu yake tsakanin 14-24 ke fama da matslar cin zarafi wanda ya hada da duka ,tsangwama zagi da fyade tsakanin ma'aUrata tare da cin mutunci da sauransu.

Shugabar hukumar kare hakkin dan adam kuma mai kula da shiyyar arewa maso yamma barista Hauwa Salihu Jauro ta ce daga watan junairun wannan shekara kawo yanzu sun samu matsalolin mata 50.

Kamar yadda masana ke fadi dai cin zarfi na tarwatsa gida ,kuma babu wanda ya cancanci cin zarfi ,domin kuwa baya ga tarwatsa gidan da yake yi baya tsaya akan wanda abin ya shafa kadai yana da tasiri ga alumma baki daya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG