Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wajen Taimakon Haihuwa Likita Yayi Sanadin Mutuwan Jariri


Mideast Israel Mozart Effect
Mideast Israel Mozart Effect

Wani likita da malamar jinya sun kashe wani jariri, likita mai suna Tayyaba Iqbal da Madhuri, sun yima wata mata aiki wajen ciro jariri a cikinta, rahotanni da suka bayyanar da cewar, likitan da mataimakiyar shi, sun saka wani abu mai kamar zobe a kafafun yaron, da kokarin jawo yaron daga cikin-cikin mahaifiyar shi.

Hakan dai ya faru ne a yankin Arewa na kasar India, wasu likitoci sun bayyanar da yadda aka gudanar da haihuwar yaron, ya sabama yadda aikin likitancin ya tanada. Wanda a dalilin haka ne yasa yaron ya mutu. Tun bayan mutuwar jaririn likitan da mataimakiyar shi sun gudu, amma ya zuwa yanzu suna hannun hukumomi, kuma za’a gurfanar dasu gaban kuliya.

A tabakin jami’in ‘yan-sanda Mohammad Tariq, ya kamata mutane su san irin likitocin da suke ziyarta, domin wasu ba sanin aikin sukayi ba, sunayin hakan ne kawai don neman abun duniya. Wasu kuma kawai ‘yan gyara samun sa’a ne. Haka kuma akwai bukatar hukumomi su zurfafa bincike a kan wadanda suka kamata su dinga duba lafiya mutane, don gujema irin wannan barnar.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG