Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kama Sojan Da Ya Harbe Matashi A Kaduna Abin A Yaba Ne - Atiku


Atiku Abubakar (Instagram/ Atiku Abubakar)
Atiku Abubakar (Instagram/ Atiku Abubakar)

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya yabi rundunar sojin Najeriya da ta bayyana kama sojan da ake zargi da harbe wani matashi mai shekaru 16 a Zaria da ke jihar Kaduna.

Atiku wanda ya nuna alhininsa kan yadda matashin ya rasa ransa, ya ce akwai bukatar a gudanar da bincike kan sauran zargin abubuwan da a jami’an tsaron suka yi a sassan kasar a lokacin zanga-zangar.

“Ina kuma kira da a gudanar da cikakken bincike a kan sauran ayyukan da sojoji, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro suka yi a lokacin zanga-zangar.” Atiku ya ce a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.

“Matakin tsare wannan soja kan wannan abin takaici abin a yaba ne kuma zai bude babin tabbatar da adalci da bin doka.” Atiku ya kara da cewa.

Tsohon mataimakin shugaban na Najeriya ya kara da cewa “na sha ba shugabannin soji da kwamandoji shawara kan su daina ba da umarni kai hari kan masu zanga-zanga.”

A ranar 6 ga watan Agusta, wani soja ya harbe wani matashi mai suna Ismail Muhammad a yankin Samaru da ke Zaria a lokacin ana zanga-zangar tsadar rayuwa.

Rundunar sojin kasar ta ce sojan ya je yin harbin gargadi ne a lokacin da harsashin ya samu matashin.

Wasu rahotanni da dama sun ruwaito cewa mutanen da abin ya faru a gabansu sun musanta hakan.

A ranar Talata, rundunar sojin ta ce an kama sojan ana kuma gudanar da bincike kan lamarin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG