Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Jinyar Yara Shida Daga Cikin Daliban Kuriga Da Aka Kubutar

Daliban Makaratar Kurigan Da Aka Kubutar
Daliban Makaratar Kurigan Da Aka Kubutar

Dalibai shida na makarantar Kuriga da aka kubutar daga hannun masu garkuwa da mutane suna jinya a Kaduna, kamar yadda rundunar sojin ta bayyana a jiya.

WASHINGTON, D. C. - An mika dalibai dari da talatin da daya daga cikin sauran su ga gwamnatin jihar.

Daliban Makaratar Kurigan Da Aka Kubutar
Daliban Makaratar Kurigan Da Aka Kubutar

Manjo Janar Mayirenso Saraso ne ya mika yaran ga gwamnan jihar Kaduna Uba Sani a madadin hedikwatar tsaro (DHQ).

Ya ce sojoji sun yi amfani da hanyoyin masu dubaru da ba na dubaru wajen ganin an sako su daga hannun masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara inda aka kai su.

Ya tabbatar da cewa yara shida namiji daya da mata biyar suna kwance a asibitin sojoji na Darlet Barracks.

Daliban Makaratar Kurigan Da Aka Kubutar
Daliban Makaratar Kurigan Da Aka Kubutar

Yaran dai sun shafe kwanaki 16 tare da wadanda suka sace su. An yi tattaki mai nisa daga jihar Kaduna zuwa makwabciyarta ta Zamfara da su a kafa.

Gwamnatin tarayyar Najeriya dai ta ce an samu nasarar sako yaran da aka sace ba tare da biyan kudin fansa ba.

Yaran wadanda aka sada su da iyayensu a wajen liyafar cin abincin da daddare, an shirya yi musu jinya a cibiyar mata da yara ta jihar Kaduna kafin a mayar da su Kuriga.

Daliban Makaratar Kurigan Da Aka Kubutar
Daliban Makaratar Kurigan Da Aka Kubutar

Daliban 131, wadanda suka isa da misalin karfe 2:07na rana a cikin motoci kirar Hiace masu dauke da kujeru 14, sun bayyana lafiyayyu, sai dai wasu daga cikin su suna dingishi sakamakon raunuka a kafa da ake imanin sun samu bayan tafiyar a cikin dajin.

An kuma sa musu sabbin riguna da takalmi da hukuma ta ba su.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG