Wata majiya daga ofishin rundunar sojin ruwa da ke jihar, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin bisa sharadin sakaya sunanta, ta ce jami’in sojan, mai mukamin Laftanar da aka bayyana sunansa da Ozuowa, rudunar soja ta ceto shi ba tare da biyan kudin fansa ba.
Jami’in sojan da lamarin ya rutsa da shi, wanda a halin yanzu yake aiki a Jirgin ruwan sojojin Najeriya (NNS) Ologbo, an bada rahoton sace shi a ranar Lahadi a Upper Iweka da ke birnin da misalin karfe 6:30 na yamma tare da wasu fararen hula da ba a tantance adadinsu ba.
Ozuowa yana kan hanyar wucewa ne daga Portharcourt, babban birnin jihar Rivers bayan an bashi izini tafiya a ranar Juma’ar da ta wuce don halartar wani dogo kwas da zai yi a lokacin da lamarin ya faru.
Majiyar ta ce “An yi masa kwantan bauna tare da wasu mutane a Upper Iweka a Onitsha. Nan take an tura dakarun gaggawa (QRF) zuwa wurin.”
Bisa ga bayanan da jaridar The Nation ta tattaro, an baza sojojin Najeriya a wuraren shiga da fita daga jihar, musamman a garin Onitsha da kewaye, inda suka tsaya da bincike bayan faruwar lamarin.