Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Garin Shelleng A Jihar Adamawa Ya Samu Sabon Sarki


Sabon sarkin Shelleng mai daraja ta daya Dr. Abdullahi Isa Dasong
Sabon sarkin Shelleng mai daraja ta daya Dr. Abdullahi Isa Dasong

Makwanni da rasuwan sarkin Shelleng a jihar Adamawa, marigayi Abdullahi Managina sarki mai daraja ta daya ,wato biyo bayan doguwar rashin lafiyar da yayi fama da shi, yanzu an nada sabon sarki don maye gurbin sarkin da ya rasun.

A takardar sanarwar nadin sabon sarkin,kwamishinan yada labaran jihar Adamawan,Comrade Ahmad Sajo,yace gwamnan jihar ya amince da zabin da masu zaben sabon sarki suka yin a zabin Dr Abdullahi Isa Dasong a matsayin sabon sarki mai daraja ta daya.

Kafin ma dai wannan sabon mukamin Dr Abdullahi Isa Dasong, shine hakimin cikin garin Shelleng,da kuma sabon nadin nasa ya zama sarki na 21 a cikin jerin sarakuna Shelleng.

Baya dai ga yan kabilar Kanakuru,wanda su ke Sarauta, haka nan akwai wasu kabilu a yankin da suka hada da Lala,da Fulani kitaku,da libo, kana kuma da sauran kabilun da aiki ko kasuwanci ya kawo su.

Yanzu haka dai Sabon sarkin da aka nada,na fa cikin farin ciki tare da mika godiyarsa dangane da hayewa kujerar da yayi,yayin da suma al’umman masarautar ke fatan alheri.

Ya dai zuwa lokacin aiko da wannan rahoto ba’a samu korafi ko tashin hankali ba, inda shugaban karamar hukumar Shelleng din Hon.Sha’aban Isa Dasong ya yaba da kai zuciya nesa da aka nuna.

Kuma tuni aka fara shirye-shiryen saka ranar baiwa sabon sarki sanda,yayin da garin Shelleng ke cigaba da daukan harami domin wannan bikin dake tafe.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG