Yanzu majalisar tayi karin haske akan ainihin dalilin da ya sa ta dakatar da tantance Ibrahim Magu ya zama shugaban hukumar EFCC.
Mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar Sanata Bala Ibn Na'Allah yace akwai abubuwa guda biyu da suka faru. Na daya yace akwai wasika da hukumar DSS ta rubuto zuwa garesu wadda yace ba daidai ba ne su juyawa wasikar baya. Kuma yace ba daidai ba ne ace wanda shugaban kasa ya turo masu basu tantanceshi ba. Saboda haka suka yanke shawarar komawa wurin shugaban kasa domin neman shawara.
Akan kasafin kudin dake gabansu Sanata Na'Allah yace majalisar zata dawo bakin aiki goma ga watan Janairu kuma daga wannan lokacin cikin mako ukku sun gama aikinsu akan kasafin kudin.
Akan kasafin kudin wannan shekara dake shudewa Sanatan yace gwamnati tayi kokari bisa ga kudaden da suka shigo mata.
Ga rahoton Musta pha Nasiru Batsari da karin bayani.