Kamar yadda wadanda suka ga abubuwan da suka gudana, sun shaidawa Muryar Amurka cewa ‘yan bindiga sun gudanar da hare-haren ne a kauyukan dake kan iyakar Jihar Gombe da kuma Jihar Borno.
To sai dai rahotanni na cewa ‘yan bindigan sun rarraba kasida mai dauke da sakonni ga ‘yan Najeriya.
Wani wanda yaso a sakaye sunanshi, cewa yayi “sako uku suka bayar, wai sako daga Jama’atu Ahlil Sunna lil Da’awati wal Jihad zuwa ga al-ummar Najeriya”.
“Sako na daya yace duk wanda yake kusanta kansa da Musulunci, to ya nisanci guraren zabe idan har yana so yayi nisan kwana, domin zamu kai hare-hare akan rumfunan zabe”.
“Sai sako na biyu, duk wanda yake neman zaman lafiya, to ya nisanci taimakawa jami’an tsaro akanmu, kuma kar ya yake mu.”
“Sannan na uku kuma na karshe, muna kiranku, kuzo kuyi Jihadi, kuma kuyi shari’ar Musulunci domin Allah Ya wajabta mana haka, gaba dayanmu.”
Wasu mazauna birnin Gombe sun bayyana abubuwan da suka gani.
“Sun shiga cikin Gombe, tabbas sun shiga duk sun mamaye ta, ba ruwansu da mutane amma sun shiga gari. Muna tsaye muna kallonsu, suna ta kabbara. Idan sun ga mota mai kyau su kwace. Yanzu haka suna wajen barikin sojoji suna ta harbi”, a cewar wani mazaunin birnin Gombe wanda baya so a bayyana sunanshi.
A halin yanzu dai, bayanai na nuna cewa ‘yan bindigan sun ja da baya, sannan Muryar Amurka yayi kokarin jin ta bakin hukumomin tsaro a Jihar, amma babu nasara.