Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Jonathan Ya Tsallake Rijiya da Baya a Gombe


Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a Gombe, Fabrairu 2, 2015
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a Gombe, Fabrairu 2, 2015

Mutane uku ne suka mutu sanadiyar bom din da ya tashi kusa da wurin da shugaba Jonathan yayi gangamin zabe.

Bom din ya tashi ne jim kadan bayan an tashi daga taron zaben da shugaba Jonathan ya gudanar a garin Gombe.

Tun farko shugaba Jonathan ya bayyana jin dadinsa dangane da irin tarbar da aka yi masa a jihar Gombe. Yace jihar Gombe jihar PDP ce an jima ana aiki da ita. Shugaban ya yiwa jihar alkawarin inganta harkokin noma, samar da takin zamani da gina jami'ar gwamnatin tarayya.

Shi ma mataimakin shugaban Namadi Sambo ya yiwa jihar albishir cewa za'a sa wutar lantarki a Dadin Kowa kana a inganta noman rani a jihar.

Saidai suna gama jawabansu wata 'yar kunar bakin wake ta tayarda bom wanda ya kashe akalla mutane uku da jikata wasu da dama.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad.

Shugaba Jonathan Ya Tsallake Rijiya da Baya a Gombe - 2'34"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG