A wata hira da Muryar Amirka tayi da shi jiya Litinin a ma'aikatar harkokin wajen Mr Kerry yace gwamnatin Amirka tana nazari sosai tana duba yiwuwa aza takunkunmin, kodayake ya fito takamame ya fadi wanda Amirka zata auna ba.
Yace yayi imanin cewa fadan da ake yi a kasar Sudan ta kudu da ya yiwo asali daga rikicin mai da neman iko da kuma gabar kabilanci ya bude da zama wani abu dabam.
A tsakiyar watan disamba fada ya barke lokacinda shugaba Salva Kir ya zargin tsohon mataimakinsa Reik Machar da laifi kokarin yi masa juyin mulki. Joh Kerry yace rikicin na kasar Sudan ta kkudu bala'i ne, musamma idan aka yi la'akari da yadda kasa ta dade tana fafitukar ganin ta samu yancin ci gashin kai.
Gobe Laraba idan Allah ya kaimu sakataren harkokin wajen na Amirka zai fara ziyara a kasashen gabashin Afrika. Zai je Addis Ababa baban birnin kasar Ethiopia inda shawarwarin da ake yi tsakanin wakilan gwamnati dana yan tawayen kasar Sudan ta kudu suka kasa samun ci gaba.