Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Kakabawa Wasu Kungiyoyin Kasar Iran Uku Takunkumi


 Steven Mnuchin, Sakataren Baitulmalin Amurka
Steven Mnuchin, Sakataren Baitulmalin Amurka

Jiya Laraba sakataren baitulmalin Amurka ya kakabawa wasu kungiyoyin kasar Iran uku da da mutane shida akan zargin suna keta hakkin jama'a a madadin gwamnatin kasarsu

A yayinda Amurka ta gabatar da shawarar a azawa jami’an kasar Sudan ta kudu takunkunmi, ta wani gefen kuma gwamnatin Amurkan ta kakabawa wasu kungiyoyin kasar Iran guda uku da wasu ‘yan Iran din guda shidda sabbin takunkunmi bisa zargin cewa sun keta hakkin jama’a a madadin gwamnatin Iran.

Kungiyoyin da aka azawa takunkunmi kamar yadda sanarwar ma’aikatar kudin Amurka ta gabatar a jiya Laraba sun hada da wata kungiyar yakin sa kai mai suna Ansar e Hizballah wadda ke goyon bayan gwamnantin kasar da gidan yarin Ewin da kuma wani kamfanin waya.

A wani jawabi da ya gabatar a ranar ashirin da daya ga watan Maris, sakataren harkokin wajen Amurka ya ce gwamnatin shugaba Trump tana shirin azawa kasar Iran takunkumi mafi gauni a tarihi, sai fa idan Iran din ta yi na’am da bukatun Amurka na dakatar da shirin kokarin kera makaman nukiliya.

To amma Iran ta musunta cewa tana kokarin kera makaman nukiliya, harma shugaban addini na kasar Ayatollah Ali Khameni, yayi watsi da kashedin da Amurka ta yiwa kasar yana mai fadin cewa Amurka ba zata yi nasara akan duk wasu take taken ta gameda kasarsa ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG