Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tilas A Gaya Mana Abunda Trump Da Putin Suka Kulla Cikin Sirri -Sanatocin Amurka.


Shugaba Trump tare da takwaransa na Rasha a taron manema labarai bayan ganawarsu a Helsinki.
Shugaba Trump tare da takwaransa na Rasha a taron manema labarai bayan ganawarsu a Helsinki.

Kare taron kolin da yayi da shugaban Rasha Vladimir Putin, a birnin Helsinki da shugaba Trump yake yi, bai kashe fusatar da wakilan majalisar dokokin Amurka suka yi ba, inda a jiya Laraba, wakilan suka bukaci bayani daga bangaren zartaswar, tare da gabatar da kudrori masu tsauri da zasu ladabtar da Rasha.

"Amurkawa da wakilan wannan kwamiti suna bukatar a fada musu abunda shugaban Amurka da shugabannin kasashen waje 'yan kama-karya, suka amince a kai cikin sirri," inji Senata Bob Menendez.

Menendez, daga jihar New Jersey, dan jam'iyyar Democrat mafi girma a kwamitin kula da harkokin kasshen waje.

"Kafofin yada labarai masu alaka d a fadar Kremlin a yanzu suna fidda karin bayanai fiyeda abunda ni dan Democrat mafi daukaka a wannan kwamiti, da sauran wakilan wannan kwamiti da Amurka suka sani," Menendez ya fada.

Ana sa ran sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo zai bayyana gaban kwamitin makon gobe. Shuaban Kwamitin, dan Republican Bob Corker, mai wakiltar jihar Tennessee a majalisar dattijan, yace, ba 'yan jam'iyyar Democrat ne kadai suke bukatar a yi musu bayani ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG