Kwamitin sulhu na Majalisar dinkin Duniya yayi Allah wadai da bijirarrun sojojin kasar Mali da suka kwace mulki daga hanun gwamnatin da aka zaba ta fuskar demokuradiyya.
A cikin sanarwa da ya bayar a yammacin jiya Alhamis, kamitin yayi kira ga sojojin su tabbatarda lafiyar shugaba Amadou Toumani Toure, kuma su koma bariki.
Haka kuma kwamaitin na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci sojojin su saki dukkan jami’an kasar Mali da suka kama, da kuma sake maido da tsarin mulkin Demokuradiyya da gwanatin kasar Mali.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon yayi kira ga wadanda suka yi juyin mulki su kiyaye daukan mataki da zai kara tarzoma cikin kasar wadda zai kara wargaza kan kasar.
A jiya Alhamis gungun wasu sojoji suka bada sanarwa ta talabijin cewa sun kaddamarda juyin mulki, bayanda suka kama kafofin yada labarai da kuma fadar shugaban kasa.
Sojojin suka ce sun dauki wan nan matakin nen domin shugaban kasar ya nuna gazawa wajen yakar ‘yan tawaye abzinawa daga arewacin kasar.
Amurka ma ta shiga sahun kasashe dake Allah wadai da wan nan juyin mulki, daga nan tace tana nazarin tsaida baiwa kasar tallafi da basu shafi ayyukan jinkai ba, da suka hada da na tattalin arziki, tsaro da kuma kudade domin yaki da ta’addanci.