Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Tsaurara Matakan Ba 'Yan Gudun Hijira takardar Bisa


Donald Trump
Donald Trump

Gwamnatin Shugaba Trump na tsaurara matakan baiwa ‘yan gudun hijira damar shiga Amurka, ta hanyar binciken kwakwaf ga masu neman shigowa daga kasashe 11 da ake ‘dauka a matsayin masu tsananin hadari.

Jami’ai sun ki bayyana sunayen kasashen masu tsananin hadarin lokacin da suka kira manema labarai domin bayyana wannan canji, amma anyi ta bayyana kasasen a rahotanni. Kasashen sun hada da Masar da Iran da Iraqi da Libiya da Mali da Koriya ta Arewa da Somaliya da Sudan ta Kudu da Sudan da Syria da kuma Yamal.

Wani jami’i ya ce banbanci ‘daya da za a gani shine yiwa mutanen da suka fito daga kasashen tambayoyi masu zurfi, sabbin matakan da aka ‘dauka zasu shafi kasashen da ke cikin jerin sunayen, kuma zai iya haifar da jinkiri ga wasu masu shiga kasar. Ana kyautata tsammanin yawancin sauye-sauyen da aka yi zasu fara aiki zuwa karshen watan Maris, a cewar wani jami’i.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG