Shugaban Amurka Donald Trump zai ci gaba da kare dokar da ya fitar a wajajen karshen watan daya, wacce ta takaita balaguron 'yayan wasu kasashe bakwai zuwa Amurka, dokar da aka yiwa kwaskwarima, kuma aka jin gwamnati zata kammala aiki akan dokar cikin kwanaki masu zuwa, inji mataimakin shugaban Amurka Mike Pence.
Mataimakin shugaban kasa Pence wanda ya bayyan ahaka a shirin talabijin na CBS jiya Laraba, yace ba wai kadai shugaban zai ci gaba da kare matakin da ya dauka tun farko a gaban kotuna ba, sun hakikance cewa matakin d a shugaban na Amurka ya dauka yana karkashin ikonsa.
Kotunan Amurka sun takawa dokar birki, wacce ta hana 'yan kasashen Iraqi, da Iran, da Libya, da Somalia, da Sudan,da Syria da Yemen zuwa Amurka. Hakan nan dokar ta dakatar da shirin karbar 'yan gudun hijira zuwa Amurka.
Fiyeda kararraki daban daban har 27 aka shigar gabvan kotunan Amurka kan wannan batu.
Facebook Forum