“Shugabar na USAID wato Gayle Smith yace, “Amurka na taimakawa ‘yan kasar ta Habasha ne saboda su rage radadin wannan matsala ta yanayin dumamar teku da ke haifar da matsaloli a nahiyar game da abinci da makamantansu”.
Ta sanar da haka ne a wata sanarwa a jiya Lahadi, inda ta ci gaba da bayyana yadda wannan dumamar tekun ta shafi amfanin gonar da hakan ya kawo karancin abinci da kara tsadar rayuwar yau da kullum ga talakawa.
Cikin taimakon har da abincin da ya kai Ton 176,000 da za a rabawa jama’a.