A cewar mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka John Kirby. Yace “zasu duba wannan lamari, kuma zasu dauki kowanne irin matakan da suka kamata idan da bukatar hakan, ko matakin MDD ko nasu na kashin kanuu.”
Mr. Kirby yace sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya tada batun wa ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif, a yammacin jiya Laraba
Iran tace makaman guda biyu na dauke da wani sako da aka rubuta da yaren Hebrew wanda ke cewa, “Kamata yayi a goge Isira’ila daga littafin tahiri.”
Kamfanin dillancin labarai na Farisa da ake cewa (FARS), ya nuna hotunan dake cewa an harba makaman ne daga dutsen Alborz dake gabashin Iraki, da manufar tafiyar nisan kilomita 1,400 daga gabar tekun kasar zuwa tekun Oman.