Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Kebe Dala Miliyan 176 Don Aiyukan Agaji A Yammacin Afirka


 Kathleen FitzGibbon
Kathleen FitzGibbon

Kasar Amurka ta sanar da ware karin miliyoyin dala domin tallafa wa al’umomin da ke bukatar agaji a kasashen yammacin Afrika.

Matsalolin tsaro da karancin abinci da yawaitar kaurar jama’a daga matsugunansu sun haddasa yanayin bukatar agajin gaugawa a wannan yanki lamarin da ya sa Amurka, ta hanyar hukumar USAID, yanke shawarar tsara aiyukan jin kai da za a gudanar da hadin guiwar kungiyoyin cikin gida da na kasa da kasa.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Ofishin Jakadancin Amurka a Nijar ta aikewa manema labarai.

An ruwaito sanarwar ta na cewar Amurka ta amince ta bayar da dala miliyan 176 saboda taimakawa al’umomin da ke cikin halin bukata a kasashen Sahel da na yankin tafkin Chadi inda matsalolin tsaro da tashe tashen hankula suka yi sanadin ficewar miliyoyin mutane daga garuruwansu na asali.

Sanarwar ta kara da cewa adadin mutanen dake bukatar agajin gaggawa ya karu a wani lokacin da isar da tallafi ke zama jidali sakamakon rigingimun da ake fuskanta a wasu yankunan kasashe irinsu Mali, Mauritania, Nijar, Burkina Faso, Kamaru, Chadi da Najeriya.

Shugaban kungiyar Kulawa Da Rayuwa, Hamidou Sidi Fody, ya yaba da wannan yunkuri koda yake kuma a cewarsa cimma nasarar wannan abu na bukatar zuba ido.

Hukumar USAID ce ke da nauyin wannan gagarumin aiki, za kuma a yi zubin kudaden gudanar da shi ta hanyar abokan huldar MDD da kungiyoyi masu zaman kansu irinsu WFP da UNICEF da OCHA domin samar da abinci da ruwan sha mai tsafta da kiwon lafiya da samar da kariya ga mutanen da ke rauni da dai wasu karin tallafi masu mahimmanci inji sanarwar.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG