Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Kaddamar Da Wasu Shirye-shirye Guda Uku Akan Al'adu Da Ilimi A Najeriya


Mataimakiyar sakatarin al’adu da ilimi a ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka, Lee Satterfield
Mataimakiyar sakatarin al’adu da ilimi a ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka, Lee Satterfield

Mataimakiyar sakatarin al’adu da ilimi a ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka, Lee Satterfield, ta bayyana haka ne a jami’ar Legas a ranar Laraba inda ta bayyana manufofin kasashen waje kan sabbin shirye-shiryen.

WASHINGTON, D. C. - Mataimakiyar sakatarin al’adu da ilimi a ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka, Lee Satterfield, ta bayyana haka ne a jami’ar Legas a ranar Laraba inda ta bayyana manufofin kasashen waje kan sabbin shirye-shiryen.

Ziyarar ta ta biyo bayan ganawar da Shugaban Amurka Joe Biden ya yi da shugabannin Afirka a birinin Washington DC a shekarar 2022 da kuma ziyarar Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, wanda ya kai Najeriya a farkon watan Janairu.

Satterfield ta sanar da kaddamar da shirin African Creative Initiative (in TV) a Talabijin TV, da shirin American Music Mentorship Programme ga waɗanda ke koyo a fannin kirkire-kirkire, da kuma Community College, inda dalibai 'yan Najeriya huɗu za su samu shiga kwalejin al'umma a Amurka.

Antony Blinken
Antony Blinken

Ta kuma sanar da kaddamar da wani fanni na samun bayannai akan jamiyoyin Amurka a UNILAG, inda dalibai za su iya samun shawarwari akan karatu a kasar da kuma hanyar samun shiga makarantun kasar da dai sauransu.

Satterfield ta ce, “Dawo wa ta nan yana da amfani don in yi magana game da fadada damammaki a tsakanin kasashenmu biyu a fannin ilimi da al’adu kuma na ambaci wasu sabbin tsare-tsare guda uku da muka kaddamar a yau; cewa akwai halin bunkasa tattalin arzikin kasa ta fanin kirkire-kirkire. Muna ganin hakan zai bada zarafin karuwa da ci gaba saboda muhimmiyar rawa da hakan ya taka a fadin duniya.

Satterfield ta kyautata zaton Shirin zai fara aiki a nan ba da jimawa ba a shekarar 2024.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG