Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta Kaddamar da Hare-Haren Jirgin Sama Akan Mayakan Daular Islama


Mayakan Daular Islama na Iraki.
Mayakan Daular Islama na Iraki.

Har yanzu madatsar ruwan Haditha wadda ke fuskantar barazana daga mayakan Daular Islama na karkashin ikon gwamnatin Iraki

Sojojin Amurka sun ce sun kaddamar da hare-haren jirgin sama a yammacin Iraki, daura da madatsar ruwan Haditha, wadda ke fuskantar barazana daga mayakan Daular Islama.

Jami'an Amurka sun fadi yau Lahadi cewa har yanzu madatsar ruwan na karkashin ikon gwamnatin Iraki ne, dama an kaddamar da harin ne don a taka burki ma mayakan sa kan, wadanda ke kokarin kwace iko da madatsar ruwan.

Da ya ke jawabi a Georgia a yau dinnan Lahadi, Sakataren Tsaron Amurka Chuck Hagel, ya ce kare Madatsar ruwan Haditha din na da matukar muhimmanci.

Sojojin na Amurka sun kuma kaddamar da hare-haren jirgin sama kan muradun 'yan Daular ta Islama a arewacin Iraki, inda su ka yi ta auna mayakan da makamansu daura da garin Irbi.

Hukumar ba da umurnin daukar matakan soji ta Amurka, ta bayyana hare-haren da cewa surki ne na nau'ukan farmaki, da jajircewar mayaka, da kuma amfani da jirage marasa matuka, wadanda aka rinka cilla su tun daga ranar Jumma'a zuwa jiya Asabar.

Kuma a Syria mai makwabtaka da Irakin, shaidu sun ce hare-haren da gwamnatin Syriar ta auna kan tungar 'yan Daular ta Islama da ke Raqqa, sun hallaka mutane akalla 25, ciki har da fararen hula 16.

Kungiyar Rajin Kare Hakkin Dan Adam a Syria, ta ce farar hulan sun mutu ne a wani harin bam da aka kai kan gidan biredin da masu tsattsauran ra'ayin ke gudanar da shi. Wasu hare-haren kuma sun dira ne kan sansanin atisaye na 'yan Daular, da kuma wani ofishin ma'aikatar kudi na gwamnati, wanda su ke amfani da shi a matsayin Kotun Musulunci.

Birnin Raqqa da ke arewa maso gabashin Syria din dai, nan ne babbar tungar kungiyar a Syria.

XS
SM
MD
LG